Brook zai yi fice a dambe a duniya -— Hearn

Kell Brook Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rabon da Brook ya yi dambe tun lokacin da aka daba masa wuka a kafarsa a Amurka

Kell Brook yana da kwarewar da zai iya zama fitaccen dan damben boksin din Birtaniya a duniya in ji mai shirya wasan Eddie Hearn.

Brook, mai shekaru 28, ya kare kambunsa na IBF ajin Welterweight ranar Lahadi, bayan da ya doke Jo Jo Dan na Romania a turmi na hudu.

Carl Froch mai shekaru 37 kuma zakaran kambun WBA ajin super-middleweight ya ce lokaci ya yi da zai yi ritaya, kuma ana hasashen Brook ne zai maye gurbinsa.

Froch wanda ya ya yi nasara a dambe 33 daga 35 da ya kara tun lokacin da ya zama kwararren dan dambe, rabonsa da dambe tun a cikin watan Mayun 2014.