Newcastle ya ci ribar fam miliyan 19 a bara

Newcastle United Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Newcastle yana matsayi na 12 a teburin Premier da maki 35

Kulob din Newcastle United na Ingila ya sanar da cin ribar fam miliyan 18.7 a kakar wasan 2013-14 kuma shekaru hudu kenan a jere yana cin riba.

Bashin da kuma ake bin kulob din yana nan a kiyasin fam miliyan 129 kuma kudin ruwane na mamallakin Newcastle Mike Ashley.

Daraktan kulob din Lee Chamley ya ce Newcastle ya samu ribar ne saboda karfin arzikin mamallakin kulob din da kuma gudunmawar da yake bayarwa.

Ya kuma kara da cewa za su kashe ribar da suka samu wajen dauko sabbin 'yan wasa da kuma fadada jarin kulob din.