UEFA ta tuhumi Montenegro da Russia

Montenegro Russia Hakkin mallakar hoto AP
Image caption UEFA ta tuhumi kasashen biyu da laifin kin kammala wasa

Hukumar kwallon kafar nahiyar Turai ta tuhumi Montenegro da Rasha bisa kin karasa wasan neman gurbin buga gasar nahiyar Turai ranar Juma'a a Podgorica.

An tsai da karawar ne bayan da aka tafi hutu, a lokacin da rikici ya barke tsakanin 'yan wasa da jami'ai, kuma tun da farko aka jefi Igor Akinfeev na Rasha da abin da ke tartsatsin wuta.

Hukumar ta tuhumi Montenegro da kin dawo wa a karasa wasa, yayin da ta tuhumi Rasha da jefa abubuwa masu tartsatsin wuta cikin fili da magoya bayan ta suka yi.

Tun farko Rasha ta mika bukatarta ga hukumar cewar a ba ta nasara a wasan duk da cewar ba a kammala ba.