Southampton ya ci ribar fam miliyan 33

Southampton Stadium Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Southampton ta ci ribar ne a karin kudin kallon wasanninta a talabijin

Kulob din Southampton ya ci ribar fam miliyan 33.4 a bara, karon farko tun lokacin da ya sayar da hannun jarinsa a shekarar 2009.

Southampton wanda ke buga gasar Premier ya sanar da cin ribar da ya samu ne daga ranar 30 ga watan Yunin 2014, wanda a shekarar 2013 ya sanar da faduwar fan miliyan 7.1

Kulob din ya ci ribar ne da karin kaso da ya samu a nuna wasanninsa a gidajen talabijin daga fam miliyan 71.8 zuwa fam miliyan 106.

Cikin ribar da kulob din ya ci bai hada da kudin da ya samu wajen sayar da Adam Lallana da Dejan Lovren da Rickie ga Liverpool da Luke Shaw da Manchester United da Calum Chambers zuwa Arsenal ba.