Tunisa ta kauce wa hukuncin CAF

Tunisia Team Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan wasan Tunisia sun yi kokarin lakada wa alkalin wasa duka

Tunisia ta bai wa CAF hakuri ta kuma kauce wa hukuncin dakatar da ita buga gasar kofin Afirka, bisa zargin da ta yi wa hukumar cewar ta nuna banbanci.

Tunisia ta yi wannan zargin ne sakamakon bugun fenaritin da aka bai wa Equatorial Guinea ta kuma lashe wasan da ci 2-1 a wasan daf da na kusa da karshe.

Sai dai kuma CAF ta ki janye tarar dala 50,000 da ta ci tawagar kwallon kafar kasar sakamakon ta da yamutsi da 'yan wasanta suka yi a wasan.

Bayan da aka tashi daga wasa ne 'yan kwallon Tunisia suka yi kokarin lakada wa alkalin wasa Rajindraparsad Seechurn duka.

Bayan da aka kammala wasan hukumar kwallon kafa ta CAF ta kuma dakatar da alkalin wasan watanni shida.