UEFA za ta raba biliyan 2 ga kungiyoyinta

Chelsea Team Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption UEFA ta ce daga gasar badi za ta raba kudaden ga kungiyoyin

Kungiyoyin da ke buga gasar cin kofin zakarun Turai da wadan da suke buga Europa League za su raba yuro biliyan 2.24 a gasar badi.

Hukumar kwallon Turan za ta kara kudin gudanar da gasar da zai kai yuro biliyan 1.66.

Hakan na nufin hukumar za ta raba kudin dai-dai wa dai-da da kungiyoyin da suke buga wasan shiga gurbin Europa League.

Kungiyoyi 32 da za su buga wasannin rukuni a gasar kofin zakarun Turai za su raba fam miyan 872 a inda kungiyoyi 48 na Europa League su raba fam miliyan 277 a tsakaninsu.

UEFA ta kuma ce ta amince ta bai wa kungiyar mambobin kulob kulob a kalla yuro miliyan 200 daga kudin shigar da za ta samu a gasar kofin nahiyar Turai na shekarar 2020.