Blatter zai sauya makomar FIFA — Rummenigge

Karl-Heinz Rummenigge Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Rummenigge tsohon dan kwallon Jamus mai zura kwallo a raga

Karl-Heinz Rummenigge ya ce a shirye Sepp Blatter yake ya kawo sauyi kan yadda ake gudanar da hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA.

Rummenigge, wanda shi ne shugaban kungiyoyin kwallon kafar Turai ya ce Blatter ya girgiza da irin sukar da ya fuskanta daga wurare da dama.

Tsohon dan kwallon Jamus, mai shekaru 59 da haihuwa ya kara da cewar yana da tabbacin za a samu gagarumin sauyi a hukumar ta FIFA.

Blatter mai shekaru 79 da haihuwa yana neman a sake zabensa a matsayin shugaban FIFA karo na biyar.

Ana hasashen Blatter ne zai yi nasara kan abokan takararsa Luis Figo da Michael van Praag da Yarima Ali na Jordan a lokacin zaben.