Wales ta yi murna da jan katin Komfany

Vincent Kompany Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kompany ba zai buga wasa da Wales ba a Cardiff

Tsohon dan kwallon Wales Mickey Thomas ya ce abin murna ne da aka bai wa Vicent Kompany jan kati a karawar da suka yi da Isra'ila.

An bai wa dan kwallon na Manchester City ne jan kati a karawar da suka doke Isra'ila da ci daya mai ban haushi a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai.

Sakamakon haka Kompany ba zai buga karawar da Belgium za ta yi da Wales a Cardiff ranar 12 ga watan Yuni ba.

Thomas ya ce rashin dan bayan a tawagar Belgium zai taimaka wa Bale da Ramsey da Allen su samu kyakkyawan sakamako a wasan.