Sterling ya ki sabunta kwantiragi da Liverpool

Raheem Sterling Hakkin mallakar hoto
Image caption Sterling ya koma Liverpool a shekarar 2010 daga QPR

Raheem Sterling ya ki ya sabunta kwantiraginsa da Liverpool duk da tayin fam 100,000 da za ta dinga ba shi a kowanne mako.

Dan kwallon ya ce ba zai tattauna da mahukuntan Liverpool kan ci gaba da zamansa a kulob din ba, har sai an kammala gasar bana duk da tayin kudin da aka yi masa.

Sterling ya kara da cewa ba maganar kudin da Liverpol zai ba shi ba ne, ya dade yana tunanin lashe kofuna a kai-a kai.

Kwantiragin dan kwallon da Liverpool zai kare nan da shekaru biyu masu zuwa, kuma yana karbar fam 35,000 a duk mako.

Rabon da Liverpool ya dauki kofi tun a shekarar 2012, lokacin da ya doke Cardiff City a bugun fenariti ya dauki League Cup.