Kila Scotland ta buga wasa ba 'yan kallo

Georgia  Scotland Hakkin mallakar hoto sns
Image caption Sai a watan gobe ne Scotland za ta san makomar wasan da za ta yi

Ranar 21 ga watan Mayu ne Scotland za ta san matsayin karawar da za ta yi a Geogia ko za ta yi ba tare da 'yan kallo ba.

Hukumar kwallon kafar Turai za ta zauna taro a watan gobe, domin hukunta Geogia kan yamutsin da ya barke a karawar da suka yi da Jamus a Tbilisi ranar Lahadi.

Sau biyu 'yan kallo na shiga filin wasa a lokacin da Jamus ke cin Georgio 2-0 a wasan neman shiga gasar cin kofin nahiyar Turan.

Haka kuma UEFA za ta yanke hukunci kan tawagar kwallon kafar Poland da Jamhuriyar Ireland da suke buga wasa a rukuni na hudu.