Ya kamata a rika yaba wa kwallon Afirka — Blatter

Sepp Blatter Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Blatter yana neman shugabancin kujerar FIFA karo na biyar a jere

Shugaban hukumar kwallon kafar duniya FIFA, Sepp Blatter, ya ce ya zama wajibi duniyar kwallon kafa ta jinjina wa nahiyar Afirka.

Shugaban ya yi wannan tsokaci ne a mujalar FIFA wacce take fita kowanne mako.

Ya kara da cewar kwarewa da jajircewar tawagar kwallon kafar kasashen da suka wakilci Afirka a kofin duniya sun kara kayata gasar.

Blatter, wanda ya ke fatan a sake zabarsa a matsayin shugaban hukumar Fifa karo na biyar a watan Mayu, zai halarci taron hukumar kwallon kafar Afirka da za ta yi a mako mai zuwa.

Blatter, mai shekaru 79 da haihuwa, ya samu gagarumar gudunmawa daga Afirka a zango hudu da ya yi yana mulkin FIFA.