Bakar fata kan wahala wajen samun aikin kociya

Chriss Ramsey Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption QPR na mataki na 19 a teburin Premier da maki 22

Kociyan QPR Chris Ramsey ya ce kasancewarsa bakar fata zai yi masa wahala ya sake samun aiki da zarar ya bar Loftus Road.

Ramsey, mai shekaru 52, ya samu damar jan ragamar QPR har zuwa karshen kakar wasan bana, bayan da Harry Rednapp ya ajiye aikin.

Ramsey ya kwashe watanni bakwai kafin ya samu aiki da QPR, bayan da ya bar Tottenham a watan Yunin 2014.

Kociyan ya ce samun aiki yana da wahala, amma bakar fata ya fi shan wahala kafin ya samu aikin musamman horar da 'yan wasan kwallon kafa.