Crystal Palace ya ci ribar fan miliyan 23

Crystal Palace
Image caption Crystal Palace yana mataki na 11 a teburin Premier da maki 36

Kulob din Crystal Palace ya ci ribar fam miliyan 23 a karon farko da ya dawo buga gasar Premier, bayan da ya biya haraji.

Kulob din ya koma buga gasar Premier ne a shekarar 2013, kuma a lokacin ya sanar da cin ribar fam miliyan 3.5.

Palace ya ci ribar ne a karshen hada-hadar watan Yunin 2014, kuma ya samun karin kudin nuna wasanninsa a talabijin da ya kai fam miliyan 74.1.

Ribar da kulob din ya samu a kakar wasan 2013-14 ya kashe ta wajen sayo 'yan wasa ciki har da yin hayar Alan Pardew daga Newcastle.