Wenger da Pulis sun kalubalanci FA

Greg Dyke Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ingila tana son ta samu karin 'yan asalain kasar da suke buga wasanni

Arsene Wenger da Tony Pulis sun kalubalanci shirin da shugaban kwallon kafar Ingila Greg Dyke ke yi na tilasta wa kungiyoyi kara adadin 'yan asalin Ingila a lokacin wasa.

Dyke yana bukatar a kara yawan 'yan wasan Ingila a kulob daga takwas su koma 12 a manyan kungiyoyin da suke buga manyan gasar kasar.

Wannan tsarin da shugaban ke son a aiwatar ya samu goyon baya daga manyan tsoffin kociyoyin Ingila biyar.

Wenger ya ce dan kwallo ne ya kamata ya nuna kansa a saka shi a wasa, shi kuwa Pulis cewa ya yi matsalar a kungiyoyin matasan 'yan wasan Ingila ta ke.

A kakar wasan bara kaso 32 cikin dari na 'yan wasan Ingila suka buga gasar Premier idan ka kwatanta da kaso 70 cikin dari da suka buga wasannin a shekaru 20 da suka wuce.