CAF ta amince ta dawo da Morocco kofin Afirka

Issah Hayatou Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hukumar kwallon kafar Afirka ta amince da hukuncin da kotun daukaka karar wasanni ta zartar

Hukumar kwallon kafar Afirka, Caf ta ce Morocco za ta kasance cikin kasashen da za su buga wasan neman gurbin shiga gasar kofin Afirka na 2017.

CAF ta amince ta dawo da Morocco buga gasar ne bayan da kotun daukaka karar wasanni ta yanke hukunci a komar da kasar cikin wasannin kofin Afirka.

A watan Fabrairu ne CAF ta yanke hukuncin dakatar da Morocco daga buga gasar kofin Afirka na shekarar 2017 da 2018 bayan kasar ta ki amincewa ta karbi bakuncin gasar 2015.

Da wannan hukuncin da aka yi yanzu, Moroocco za ta kasance cikin kasashen da za a raba jadawalin neman gubin buga gasar 2017 da za a fitar ranar 8 ga watan Afirilu a Alkahira.

Mocooco ta ki karbar bakuncin gasar kofin Afirka na 2015 bisa tsoron kada a kai mata cutar Ebola cikin kasarta.

Equatorial Guinea ce ta karbi bakuncin wasannin 2015 a inda Ivory Coast ta lashe kofin a karo na biyu bayan da ta doke Ghana a wasan karshe a bugun fenariti.