An cire dokar da ta iyakance shekarun jagorantar CAF

Issa Hayatou Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hayatou zai iya sake neman shugabancin Caf bayan 2017

Hukumar kwallon kafar Afirka (CAF) ta cire dokar da ta iyakance shekarun duk wani mai so ya jagoranci hukumar.

Dukkan mambobin hukumar 54 ne suka amince da sauya dokar wadda ta tanadi cewa duk jami'in da ya haura shekaru 70 ba zai jagoranci hukumar ba.

Tun da farko an bayar da shawarar sauya dokar ne domin ta yi daidai da ta hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA.

Da wannan sauyin dokar da aka zartar, Issa Hayatou, wanda shekarunsa 68 da haihuwa, zai iya neman ci gaba da jagorantar hukumar a shekarar 2017.

Mista Hayatou ya fara shugabantar CAF ne a shekarar 1988 kuma saura shekaru biyu ya kare mulkinsa amma yana fatan a sake zabarsa ya yi wani sabon wa'adi na shekaru hudu lokacin da zai cika shekaru 75 a duniya.