'Lokaci ya yi da za mu fuskanci Man United'

Vincent Kompany Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Manchester City tana mataki na hudu a teburin Premier da maki 61

Vincent Kompany ya ce lokaci ya yi da ya kamata su fuskanci Manchester United a gasar Premier a mako mai zuwa.

City ta sha kashi a hannun Crystal Palace da ci biyu da daya a karawar da suka yi ranar Litinin kuma hakan yasa ta koma mataki na hudu a teburin Premier.

Haka kuma City ta yi rashin nasara a wasanni uku daga cikin wasanni biyar da ta buga a baya, a inda United ta lashe wasanninta biyar a jere.

Kompany ya ce wasan hamayya na hamayya ne kuma babu maganar matakin da kungiyoyin suke a gasa.

Ranar Lahadi ne Manchester United za ta karbi bakuncin Manchester City a gasar Premier wasan mako na 32 a Old Trafford.