Sherwood na son yin aiki da Ramsey

Tim Sherwood Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Aston Villa tana mataki na 17 a teburin Premier

Kociyan Aston Villa, Tim Sherwood, ya ce yana sha'awar ya yi aiki tare da mai horar da QPR, Chris Ramsey, a kakar wasan badi.

Ramsey ya yi wa Sherwood mataimakin kociya a Tottenhama a bara, kuma aminan juna ne kafin kowannensu ya bar kulob din.

Kuma ranar Talata ne Aston Villa za ta karbi bakuncin QPR a gasar Premier wasan mako na 32 da za su kara a filin wasa na Villa Park.

Villa tana mataki na 17 a teburin Premier da tazarar maki uku tsakaninta da QPR, wacce take matsayi na 19 bayan buga wasanni 31 da suka yi.

Sherwood ya ce wannan wasan zai kasance daya daga cikin manyan wasannin da zai kara a bana domin tserar da kulob din daga barin gasar Premier a bana.

Shi kuwa Ramsey cewa ya yi bai taba tunanin za su fuskanci junansu a kwallon kafa ba, amma tunda za su hadu zai yi iya kokarinsa ya doke Aston Villa a karawar.