Barcelona ta doke Almeria da ci 4-0

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Har yanzu Barcelona tana matakinta na daya a teburin La Liga

Barcelona ta samu nasara a kan Almeria da ci 4-0 a gasar Spaniyar La Liga wasan mako na 30 da suka kara ranar Laraba.

Messi ne ya fara cin kwallon farko sai Suárez da ya ci kwallaye biyu kafin Bartra ya ci ta karshe saura minti 15 a tashi daga wasan.

Da wannan nasarar Barcelona ta lashe wasanni 20 daga cikin 21 da ta buga a baya, tana nan kuma a matsayinta na daya a teburin La Liga da maki 74.

Barcelona na fatan lashe kofuna uku ciki har da kofin Zakarun Turai da za ta buga wasan daf da na kusa da karshe da Paris St-Germain da kuma wasan karshe a Copa del Rey da Atletico Bilbao.