Juventus ta kai wasan karshe a kofin Italia

Juventus Team
Image caption Rabon da Juventus ta lashe kofin Italia tun a shekarar 1995

Mai rike da kofin Serie A Juventus ta kai wasan karshe a gasar cin kofin Italiya, bayan da ta doke Fiorentina da ci 3-0 a ranar Talata.

Juventus ta ci kwallayenta uku ne ta hannun Matri da Pereyra da kuma Bonucci, kuma a wasan farko da suka kara Fiorentina ce ta lashe karawar da ci ci 2-1.

Da wannan nasarar da Juventus ta samu za ta jira wacce za ta kara da ita a wasan karshe tsakanin Napoli ko Lazio wadan da za su fafata a tsakaninsu ranar Laraba.

Juventus, tana fatan lashe kofuna uku a kakar bana, tana mataki na daya a teburin Serie A, sannan za ta kara da AS Monaco a gasar kofin zakarun Turai wasan daf da na kusa da karshe.

Rabon da Juventus ta lashe kofin Italia tun a shekarar 1995.