Liverpool ta kai wasan daf da karshe a kofin FA

Blackburn Liverpool Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool za ta kara da Aston Villa a Wembley ranar 19 ga watan Afirilu

Liverpool ta kai wasan daf da karshe a gasar kofin kalubalen Ingila, bayan da ta doke Blackburn Rovers da ci daya mai ban haushi a filin wasa na Ewood Park.

Philippe Coutinho ne ya ci wa Liverpool din kwallo daya tilo da ta ba su damar kai wa wasan daf da na karshe a gasar saura minti 10 a tashi daga wasan.

Karawar farko da suka yi a filin wasa na Anfield tashi suka yi babu ci, dalilin da yasa aka buga wasa na biyu a gidan Blackburn Rovers.

Da wannan nasarar da Liverpool ta samu za ta fafata da Aston Villa a wasan daf da na karshe ranar 19 ga watan Afirilun nan a Wembley.