Bhullar ya zama dan India na farko a wasan NBA

Sim Bhullar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bhullar ya kafa tarihin buga NBA a inda ya yi wasa na dakika 16

Sim Bhullar ya kasance dan kwallon kwandon India na farko da ya fara buga gasar kwallon kwandon Amurka, wato NBA.

Bhullar -- mai shekaru 22 da haihuwa -- ya fara wasansa na farko ne da kungiyar Sacramento Kings wacce ya rattaba hannu a kwantiragin kwanaki 10 da ita.

Ya kuma shiga wasan ne saura sakwanni 16 a tashi karawar da Kings ta doke Minnesota Timberwolves da ci 116 da 111.

Dan wasan da aka haifa a Canada ya ce yana fatan nan gaba za a samu dubban 'yan India suna buga gasar NBA.

Haka kuma ya ji dadi da ya kasance dan India na farko da ya fara buga wasa a gasar NBA ta Amurka.