Chelsea na zawarcin Muto na Japan

Yoshinori Muto Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea tana mataki na daya a teburin Premier da maki 70

Kulob din Chelsea yana yunkurin dauko dan kwallon kasar Japan Yoshinori Muto mai wasa a FC Tokyo.

Wata kafar yada labarai a Japan ce ta ruwaito cewar zabi ya rage wa Muto idan zai iya komawa taka leda Stamford Bridge a badi.

Dan wasan mai shekaru 22 ya buga wa Japan wasanni 11, ya kuma zura kwallaye uku a raga a gasar J-League da aka fara yi.

Muto ya ci kwallaye 13 a kakar wasan bara, kuma yana daga cikin 'yan wasan 11 da aka zaba a gasar cin kofin Asia da suka kai wasan daf da na kusa da karshe.

A watan Fabrairun 2015 ne Chelsea ta kulla yarjejeniya saka riga da kamfanin yin taya na Japan da ta kai fam miliyan 40.