Ronaldo ya ci kwallaye 300 a Real Madrid

Cristiano Ronaldo
Image caption Madrid tana mataki na biyu a teburin La Liga da maki 70

Cristiano Ronaldo ya zura kwallo ta 300 a wasan da Real Madrid ta doke Rayo Vallecano da ci 2-0 a gasar Spaniyar La Liga wasan mako na 30.

Ronaldo dan wasan Portugal ya ci kwallaye 300 kenan a Madrid daga cikin wasanni 288 tun lokacin da ya koma kulub din daga Manchester United a shekarar 2009.

Kuma shi ne dan wasan Madrid na uku da ya ci kwallaye sama da 300, bayan Raul da ya ci 323 da Alfredo Di Stefano da ya ci 307.

Haka kuma dan wasan ya zura kwallaye biyar a karon farko a wasan da Madrid ta casa Granada da ci 9-1 a gasar La Liga.