Wani magoyin Liverpool ya kalubalanci Sterling

Liverpool Unvail Kit Hakkin mallakar hoto nbfootball
Image caption Liverpool za ta kara da Newcastle a gasar Premier wasan mako na 32

Wani mai goyon bayan Liverpool ya kalubalanci Raheem Sterling a lokacin da Liverpool take gabatar da sabbin kayayyakin wasa ga magoya bayanta.

Dan wasan mai shekaru 20, ya sanarwa da BBC cewar ya ki amincewa ya sabunta kwantiragin fan 100,000 a duk mako da aka yi masa tayi, har sai karshen kakar wasan bana.

Sterling yana cikin 'yan wasan da suka nuna kayayyakin da Liverpool za ta yi amfani da su a kakar badi a ranar Juma'a.

Wani daga cikin magoya bayan kungiyar ya daga murya a inda ya ce "Ka tabbata mun ganka a Liverpool a kakar badin"

Sterling ya zura kwallaye 17 daga wasanni 89 tun lokacin da ya fara buga wa Liverpool wasa a watan Maris 2012.