Muna kokarin rike Clyne a kulob dinmu -Koeman

Image caption 'Yan wasan Southampton a filin kwallo.

Kocin Southampton Ronald Koeman ya ce kulob din sa da kyar zai iya ci gaba da rike dan kwallonsa dan wasan baya Nathaniel Clyne.

Clyne wanda ke murza wa Ingila leda, ya koma kulob dinne daga Crystal Palace a watan Yulin 2015, kuma yarjejeniyarsa da kulob din za ta kare ne 2016.

A hirarsa da BBC Koeman ya ce "Har yanzu muna kokarin rike Clyne a kulob din mu. Mun kuma san sai mun yi da gaske, domin yana da masu zawarcinsa."

Ya kara da cewa, "A yanzu haka, babu wani dan kwallonmu da aka matsa wajen zawarcinsa, amma muna iya kokarin mu rike su."

Koeman kuma bai ba da tabbaci a kan makomar dan wasan baya Toby Alderweireld, wanda wa'adin aron sa daga Atletico Madrid, ya kusa karewa.