Stoke za ta sabunta kwantiragin Begovic

Asmir Begovic Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana jita-jitar cewar Asmir Begovic zai iya barin Stoke City a karshen kakar badi

Kocin Stoke City Mark Hughes ya ce suna shirye-shiryen tsawaita kwantiragin gola Asmir Begovic a karshen kakar wasan bana.

Saura shekara daya mai tsaron ragar dan kasar Bosnia-Hercegovina kwantiraginsa ya kare da Stoke kuma ana jita-jitar zai bar kulob din a badi.

Begovic, mai shekaru 27 da haihuwa, ya koma wasa a Stoke City a shekarar 2010, kuma koci Hughes yana bukatar dan kwallon ya ci gaba da wasa da su.

Kuma shi ne golan da Stoke take amfani da shi a wasanninta a inda Thomas Sorensen da kuma Jack Butland suke jiran karta kwana a benci.