Van Persie ba zai buga wasansu da Man City ba

Robin van Persie Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A wasan farko Manchester City ce ta doke United da ci daya mai ban haushi

Robin van Persie ba zai buga karawar da Manchester United za ta yi da Manchester City a gasar Premier wasan mako na 32 ranar Lahadi a Old Trafford ba.

Tuni dan wasan ya dawo atisaye bayan da ya yi jinyar raunin da ya ji a kafarsa, amma har yanzu bai koma kan ganiyarsa ba.

Shi kuwa Chris Smalling na fama da rashin lafiya, yayin da Luke Shaw yake yin jinyar rauni, Evans kuwa yana zaman hukunci sai Pereira da yake tare da tawagar Brazil yan kasa da shekaru 20.

Kyaftin din Manchester City Vincent Kompany na yin jinya amma likitoci za su duba lafiyarsa idan zai iya buga wasan hamayyar.

Wilfred Bony ma na fama da yin jinya, a inda Dedryck Boyata da kuma Stevan Jovetic ba za su buga wasan ba.

Manchester United wacce take mataki na uku a teburin Premier za ta karbi bakuncin Manchester City wacce ke matsayi na hudu a teburin ranar Lahadi a Old Trafford.