Munich ta ci gaba da zama ta daya a Bundesliga

Bayern vs Frankfurt
Image caption Munich tana mataki na daya a teburin Bundesliga da maki 70

Bayer Munich ta doke Eintracht Frankfurt da ci 3-0 a gasar Bundesliga wasan mako na 28 da suka kara a ranar Asabar.

Robert Lewansdowski ne ya zura kwallaye biyu a wasan, yayin da Thomas Muller ya kara ta uku saura minti takwas a tashi daga karawar.

Lewandowski yanzu haka ya zura kwallaye 16 a raga, kuma saura kwallaye uku ya tarar da Alexander Meier na Eintracht Frankfurt a takarar wanda ya fi zura kwallo a gasar.

Yanzu saura wasanni shida a kammala gasar bana, kuma Bayern Munich tana mataki na daya a teburi ta kuma bai wa Wolfsburg tazarar maki 13.

Ga sakamakon wasu wasannin da aka buga:

  • FSV Mainz 05 2 - 3 Bayer Leverkuzsen
  • Borussia Mönchengladbach 3 - 1 Bor Dortmund
  • Schalke 0 - 0 Sport-Club Freiburg
  • SC Paderborn 2 - 1 FC Augsburg