City ba ta ganiyar da za ta fuskanci United

Man United Man City
Image caption United tana mataki na uku a teburin Premier City na matsayi na hudu

Robie Savage ya ce Manchester City ba ta kan ganiyarta a wasan hamayya da za ta fafata da Manchester United a gasar Premier ranar Lahadi.

Savage mai sharhi kan wasanni ya kara da cewar bai kamata kyaftin din City Vincent Kompany ya ce suna cikin tagomashin da za su fuskanci United ba.

Ya kuma ce duk da City ta doke United a Old Trafford a wasanni uku a jere a baya, wannan karon suna da matsala daga masu tsaron bayansu a karawar da suka yi gida da waje.

Haka kuma doke Tottenham da Liverpool da kuma Aston Villa da United ta yi ya kara mata kwarin gwiwar fuskantar City wacce Crystal Palace ta doke ta da ci 2-1.

Ranar Lahadi ne Manchester United za ta karbi bakuncin Manchester City a gasar Premier wasan mako na 32 a Old Trafford.