Ba za mu dauki kofin Premier bana ba — Wenger

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal tana mataki na biyu a teburin Premier da maki 66

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce idan suka doke Chelsea a wasan Premier da za su fafafata bai isa a ce za su dauki kofin bana ba.

Arsenal ta samu nasara a kan Burnley da ci daya mai ban haushi, tana matsayi na biyu biye da Chelsea a teburin Premier, kuma Chelsea za ta ziyarci Emirates ranar 26 ga watan Afirilu.

Wenger ya ce "Bana tsammani karawar da za mu karbi bakuncin Chelsea shi ne zai zama wasan raba gardama a daukar kofin Premier bana, domin suna da kwanta wasa daya".

Arsenal za ta kara da Reading a gasar cin kofin FA a Wembley kafin ta fafata da Chelsea a wasan Premier wasan mako na 33 a Emirates.