Chelsea ta ci gaba da jan ragamar teburin Premier

QPR vs Chelsea Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Chelsea wacce take mataki na daya a teburin Premier ta bai wa Arsenal tazarar maki bakwai tsakani

Kungiyar Chelsea ta doke QPR da ci daya mai ban haushi a gasar Premier wasan mako na 32 da suka kara a Loftus Road ranar Lahadi.

Chelsea ta zura kwallo ne ta hannun Cesc Fàbregas saura minti uku a tashi daga wasan, bayan da ya samu kwallo daga wajen Eden Hazard.

Nasarar da Chelsea ta samu yasa ta ci gaba da zama ta daya a teburin Premier da maki 73, kuma tana da kwantan wasa daya da Leicester City.

Rabon da Chelsea ta doke QPR a gasar Premier a Loftus Road tun a shekarar 1969, bayan da ta samu nasara da ci 4-0.

Chelsea za ta ziyarci Arsenal a wasan mako na 33 ranar 26 ga watan Afirilu a Emirates.