Gareth Bale ya dawo atisaye da Madrid

Gareth Bale Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Real Madrid tana mataki na biyu a teburin La liga a Spaniya

Dan kwallon Real Madrid Gareth Bale ya dawo atisaye domin fuskantar karawa da za su yi da Atletico Madrid a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai ranar Talata.

Bale, mai shekaru 25, bai buga karawar da Madrid ta doke Eibar da ci 3-0 ranar Asabar sakamakon jinya da ya yi.

Madrid ta sanar a shafinta na Internet cewa "Bale ya yi atisaye da sauran 'yan wasa da sanyin safiyar Lahadi".

Real Madrid ce ta doke Atletico Madrid da ci 4-1 a wasan karshe na cin kofin Zakarun Turai a watan mayun 2014.

Tun kuma daga lokacin ne Atletico ta doke Madrid a gasar La Liga gida da waje da kuma 4-0 da ta yi wa Madrid ranar 7 ga watan Fabrairu a filin wasa na Vicente Calderon.