Man United to doke Man City 4-2

United vs City
Image caption United za ta ziyarci Chelsea ranar Asabar, City za ta karbi bakuncin West Ham ranar Lahadi

Manchester United ta casa Manchester City da ci 4-2 a gasar Premier wasan mako na 32 da suka buga ranar Lahadi a Old Trafford.

City ce ta fara zura kwallo ta hannun Aguero a minti takwas da fara wasa, kafin United ta farke kwallo ta hannun Young sannan Fellaini ya kara ta biyu aka tafi hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo daga hutu ne United ta kara ta uku ta hannun Mata, sannan Smalling ya zura ta hudu, kafin City ta rage kwallo daya ta hannun Aguero kuma kwallonsa ta 100 da ya ci a City kenan.

Da wannan nasarar United tana matakinta na uku da maki 65, yayin da City tana matsayi na hudu da maki 61.

United za ta kara da Chelsea a wasan mako na 33 ranar 18 ga watan Afirilu, yayin da City za ta karbi bakuncin West Ham ranar 19 ga watan Afirilu a Etihad.