Pirlo ya tashi daga jinyar da ya yi

 Andrea Pirlo Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Juventus ce ke kan gaba a kan teburin Serie da maki 70

Dan wasan Juventus Andrea Pirlo zai dawo taka leda a karawar da za suyi da Monaco a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Talata.

Tuni likitoci suka sanar da cewa Pirlo wanda ya yi jinyar makwanni bakwai ya ji sauki zai kuma iya wasa a Monaco.

Pirlo ya ji rauni ne a karawar da suka yi da Borussia Dortmund a wasan zagaye na biyu na gasar cin kofin zakarun Turai.

Sai dai tsohon dan kwallon Manchester United Paul Pogba ya ji rauni ba zai buga karawar ba.

Shima kyaftin din Monaco Jeremy Toulalan da kuma Ricardo Carvalho watakila ba za su buga wasan ba sakamakon jinyar rauni da suke yi.

Rabon da Juventus ta kai wasan daf da karshe a gasar kofin zakarun Turai tun a shekarar 2003.