Liverpool ta doke Newcastle da ci 2-0

Raheem Sterling Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Liverpool za ta kara da West Brom a wasan mako na 33

Liverpool ta samu nasara a kan Newcastle United da ci 2-0 a gasar Premier wasan mako na 32 da suka kara a Anfield ranar Litinin.

Raheem Sterling ne ya fara zura kwallo a minti na tara da fara karawar, daga baya Joe Allen ya kara ta biyu saura minti 20 a tashi daga wasan.

Newcastle wacce aka doke ta wasa na biyar a jere, ta kammala karawar ne da 'yan wasa 10 a fili, a inda aka bai wa Moussa Sissoko jan kati.

Da wannan nasarar Liverpool ta ci gaba da zama a matsayi na biyar a teburin Premier da maki 57.