Sakho zai yi jinyar makwanni hudu

Mamadou Sakho Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool za ta karbi bakuncin Newcastle United a ranar Litinin

Likitocin kulob din Liverpool sun sanar da cewar Mamadou Sakho zai yi jinyar makwanni hudu.

Hakan na nufin dan wasan dan kwallon Faransa ba zai buga wasan daf da karshe da za su buga da Aston Villa a kofin FA a Wembley ba.

Haka kuma Sakho ba zai buga wasan Premier da Liverpool za ta kara da Newcastle da West Brom da Hull City da kuma QPR ba.

Sakho ya ji raunin ne a lokacin da suka buga wasa na biyu da Blackburn a kofin FA ranar Laraba.

Liverpool na fatan dan kwallon zai warke domin fuskantar karawar da za suyi da Chelsea ranar 10 ga watan Mayu a Stamford Bridge.