"Kada a dora wa Toure laifin rashin nasara a United"

Yaya Toure Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Manchester City tana mataki na hudu a teburin Premier da maki 61

Tsohon dan wasan Manchester United Phil Neville ya ce ya san za a dora wa Yaya Toure laifin lashe su da United ta yi 4-2 a ranar Lahadi.

Neville wanda yanzu yake sharhin wasanni ya ce yadda koci Manuel Pellegrini yake buga salon wasan tsakiya ne matsalar City.

Kuma karawar da suka yi a wasan hamayya da United an mamayi City ne daga tsakiya dalilin da yasa Toure ya kasa taka rawar gani a wasan in ji Neville.

Ya kuma kara da cewar wannan wasan shi ne kuskuren da kociyan City Pellegrini yake yi a kakar wasan bana da ake doke su.

City tana mataki na hudu a teburin Premier da maki 61, kuma za ta karbi bakuncin West Ham a wasan mako na 33 ranar 19 ga watan Afirilu.