Zakarun Turai: Atletico za ta ke ce raini da Madrid

Atletico Madrid_real Madrid Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasan farko na cin kofin zakarun Turai a karawar daf da na kusa da karshe

Atletico Madrid za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan farko na cin kofin zakarun Turai wasan daf da na kusa da karshe ranar Talata.

Real Madrid ce ta doke Atletico Madrid da ci 4-1 a wasan karshe na cin kofin zakarun Turai a watan Mayun 2014.

Tun daga lokacin ne Atletico ta doke Madrid a gasar La Liga gida da waje da kuma 4-0 da ta yi wa Madrid ranar 7 ga watan Fabrairu a filin wasa na Vicente Calderon.

Madrid ta samu kwarin gwiwar tunkarar wasan bayan da Gareth Bale ya murmure daga raunin da ya yi jinya.

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce Gareth Bale yana da rawar da zai taka a kokarin da suke na kare kambunsu.

Ga sakamakon wasannin da kungiyoyin suka kara a 2014/2015.

  • Spanish Primera Liga Atl Madrid 4 - 0 Real Madrid
  • Copa del Rey Real Madrid 2 - 2 Atl Madrid
  • Copa del Rey Atl Madrid 2 - 0 Real Madrid
  • Spanish Primera Liga Real Madrid 1 - 2 Atl Madrid
  • Spanish Super Cup Atl Madrid 1 - 0 Real Madrid
  • Spanish Super Cup Real Madrid 1 - 1 Atl Madrid