"Man United za ta dauki kofin Premier a badi"

Manchester United Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption United za ta kara da Chelsea a wasan mako na 33 ranar Asbar a Stamford Bridge

Eric Cantona ya ce yadda Man United ta doke Man City wata manuniya ce da ke nuna cewar za ta dauki kofin Premier na badi.

United ta doke City ne da ci 4-2 a gasar Premier wasan mako na 32 da suka buga ranar Lahadi, ta kuma ci gaba da zama a mataki na uku a teburi.

Cantona -- wanda ya lashe kofuna hudu a United a tsakanin 1992 zuwa 1997 -- ya ce, "Yanzu an raba tsaba da tsakuwa don haka United ce kan gaban City".

Ya kara da cewar "United za ta koma kan ganiyarta za kuma ta dawo da daukar kofuna kamar yadda ta yi a baya.

Rabon da Manchester United ta doke Manchester City a Old Trafford tun a shekarar 2011.

United tana mataki na uku a teburin Premier da maki 65, yayin da City take matsayi na hudu da maki 61.