Za a binciki Sterling saboda shan kayan maye

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Sterling ne ya zura kwallon farko da Liverpool ta doke Newcastle 2-0

Kociyan Liverpool, Brendan Rodgers, ya ce zai yi magana da Raheem Sterling bayan da aka gan shi a wani hoto yana shan kayan maye.

Wani hoto da jaridar The Sun ta buga ya nuna dan wasan na Ingila mai shekaru 20 yana shan kayan maye.

Sterling ne ya zura kwallon farko kuma Joe Allen ya ci kwallo ta biyu da Liverpool ta doke Newcastle 2-0 a Anfield ranar Litinin.

Rodgers ya ce, "Ina ganin bai dace ya yi hakan ba."

Wannan lamari ya faru ne bayan Sterling ya amince cewa ya ki yarda da kwantaragin Liverpool, inda za a rika biyansa fam 100,000 a duk mako.