An samu Joss Labadie da laifin cizo a wasa

Joss Labadie Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan ne karo na biyu da aka samu dan wasan da laifin cizo

An dakarar da Joss Labadie daga buga wasanni tsawon watanni shida bisa samunsa da laifin cizo a lokacin wasa karo na biyu a shekara.

Dan wasan mai shekara 24 da haihuwa an taba hukunta shi, a inda aka hana shi buga wasanni 10 bayan da ya ciji dan wasan Torqauy United a bara.

Mai taka leda a Dagenham and Redbridge ya ki amincewa da tuhumar da aka yi masa ta cizon dan wasan Stevenage Ronnie Henry a watan Maris da ya gabata.

Hukuncin da aka yanke wa dan kwallon ya fara aiki nan take