Man United za ta kare kambunta a Amurka

USA Preseason Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Man United tana mataki na uku a gasar Premier da maki 65

Manchester United za ta kare kambunta a wasannin tunkarar gasar badi a Amurka wanda ta lashe kofin da aka fara gabatarwa a bara.

Gasar bana za ta kunshi mai rike da kofin wato United da Chelsea da Barcelona da Fiorentina da Porto da PSG da LA Galaxy da New York Red Bulls da San Jose Earthquakes da kuma Club America.

A karon farko da aka fara wasannin a bara, sama da 'yan kallo 109,318 ne suka kalli fafatawa tsakanin United da Real Madrid a filin wasa na Michigan.

United karkashin jagorancin Louis Van Gaal ce ta lashe wasannin bara, bayan da ta doke Liverpool a wasan karshe ranar 4 ga watan Agusta.

Har yanzu masu gudanar da wasannin ba su fitar da filaye da jaddawalin yadda kungiyoyin za su fafata ba a wasannin.