Ya kamata Terry ya koma buga wa Ingila wasa

Terry Capello Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An tuhumi Terry da yin kalamun wariyar launin fata

Tsohon kocin Ingila Fabio Capello ya ce ya kamata kyaftin din Chelsea John Terry ya dawo buga wa tawagar kwallon kafar kasar wasanni.

Capello ya yi ritaya daga horar da Ingila a Fabrairun 2012, bayan da hukumar FA ta cire Terry daga kyaftin din kasar, bayan da aka samu dan wasan da kalamun wariyar launin fata ga Anton Ferdinand na QPR.

An samu Terry mai shekaru 34 da haihuwa da laifi ne, bayan da kotu ta saurari karar da aka shigar a Yulin 2012, a inda aka dakatar da shi wasanni hudu da kuma tarar fam 220,000.

Terry ya buga wa Ingila wasanni 78, sannan ya yi ritaya daga buga wa tawagar kwallon kafar tamaula a watan Satumbar 2012.

Capello ya jagoranci Ingila a Disambar 2007, ya kuma koma horar da Rasha tun daga Yulin 2012.