Zaben dan kwallon da ya fi yin fice a Premier

PFA Awards Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Karo na uku kena ana zabo Hazard a cikin 'yan takarar gwarzon dan kwallon kafar Premier

An fitar da sunayen 'yan wasan kwallon kafa da za a zabo wanda ya fi yin fice a gasar Premier bana.

Cikin 'yan wasan da za a zaba sun hada da Harry Kane na Tottenham da golan Manchester United David De Gea da Eden Hazard na Chelsea.

Sauran 'yan wasan sun hada da Philippe Coutinho na Liverpool da Alexis Sanchez na Arsenal da kuma Diego Costa na Chelsea.

Karo na uku kenan da ake saka sunan Hazard a cikin yantakara, a inda Gareth Bale da Luis Suarez suka lashe kyautar a baya.

Ga jerin kyaututtuka da za a fitar da gwani

Dan kwallon da ya fi yin fice

 • Diego Costa (Chelsea)
 • David De Gea (Manchester United)
 • Philippe Coutinho (Liverpool)
 • Eden Hazard (Chelsea)
 • Harry Kane (Tottenham Hotspur)
 • Alexis Sanchez (Arsenal)

Matashin dan wasan da babu kamarsa

 • Thibaut Courtois (Chelsea)
 • Philippe Coutinho (Liverpool)
 • David De Gea (Manchester United)
 • Eden Hazard (Chelsea)
 • Harry Kane (Tottenham Hotspur)
 • Raheem Sterling (Liverpool)

Macen da ta fi yin fice

 • Eniola Aluko (Chelsea)
 • Lucy Bronze (Manchester City)
 • Jess Clarke (Notts County)
 • Karen Carney (Birmingham City)
 • Kelly Smith (Arsenal)
 • Ji So-yun (Chelsea)

Matashiyar 'yar wasan da babu kamarta

 • Freda Ayisi (Birmingham City)
 • Hannah Blundell (Chelsea)
 • Aoife Mannion (Birmingham City)
 • Nikita Parris (Manchester City)
 • Leah Williamson (Arsenal)