Za a ci gaba da gasar wasannin Turkiya

Fernebahce Bus Attack Hakkin mallakar hoto Fernabehce sk
Image caption Tun da farko Fernabehce ta ce sai an farauto wadan da suka kai harin kafin ta koma taka leda

Hukumar kwallon kafar Turkiya ta sanar da cewar za a ci gaba da gasar wasan kwallon kafar kasar wato Super Lig ranar Juma a.

Tun da farko hukumar ta dakatar da wasannin ne sakamakon kai hari da aka yi wa Fenerbahce a inda yan bindiga suka harbi motar 'yan wasa suna tafiya.

Fernebahce ta amince za ta fafata da Mersin a gasar cin kofin kalubale ranar Alhamis, bayan da mahukunta suka bayar da tabbacin za su tanadi kyakkyawan tsaro ga 'yan wasan.

Haka kuma kulob din zai kara da Bursaspor ranar Litinin a gasar wasannin kasar.

Shugaban hukumar kwallon kafar kasar ya ce 'yan ta'adda ne suka kai wa Fernebahce harin a ranar 4 ga watan Afirilu.