Djokovic ya lashe gasar Monte Carlo

Novak Djokovic Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Djokovic ya lashe wasanni 17 a shekarar 2015

Novak Djokovic ya lashe gasar kwallon tennis ta Monte Carlo bayan da ya doke Tomas Berdych da ci 7-5 4-6 6-3 a karawar da suka yi ranar Lahadi.

Djokovic ya kafa tarihin dan wasan tennis da ya lashe gasar kwararru guda uku a shekara daya, kuma ya lashe wasanni 17 a 2015.

Dan kwallon mai shekaru 27 da haihuwa ya lashe gasar Indian Wells da kuma ta Miami a watan jiya.

Djokovic wanda shi ne na daya a jerin wadan da suka fi iya wasan kwallon tennis a duniya na kuma fatan lashe gasar French Open da za a fara a watan gobe.