United na zawarcin Depay daga PSV Eindhoven

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Depay a lokacin gasar cin kofin duniya a Brazil

Zakarun gasar kwallon Holland, PSV Eindhoven sun ce Manchester United na zawarcin dan kwallonsu Memphis Depay.

Dan kwallon mai shekaru 21, shi ne ya fi kowa zura kwallaye a gasar kwallon Holland, inda ya ci kwallaye 21 sannan ya taimaki PSV ta lashe gasar a karon farko cikin shekaru bakwai.

Darekta a PSV Marce Branda ya ce "Mun samu kira a wayar salula a kansa, amma kawo yanzu bamu soma tattaunawa ba."

Depay wanda dan kasar Holland ne, shi ne ya zura kwallo ta biyu inda PSV ta doke Heerenveen da ci hudu da daya a ranar Asabar sannan ta lashe gasar.

Kungiyar PSV ta ce Depay darajarsa ta fi Euro miliyan 20.