Watakila Bale ba zai buga wasa da Atletico ba

Gareth Bale Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasan farko sun tashi babu ci ne a gidan Atletico Madrid

Real Madrid ta sanar da cewar watakila Gareth Bale ba zai buga wasan cin kofin zakarun Turai da za su buga da Atletico ranar Laraba ba.

An canja Bale, mai shekaru 25, a minti na biyar da fara karawar da Madrid ta doke Malaga da ci 3-1 a gasar La Liga ranar Asabar.

Shi kuwa dan kwallon Croatia Luka Modric ba zai buga wasan ba, sakamakon raunin da ya ji a gwiwarsa, zai yi jinyar makwanni shida.

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti yana fatan Karim Benzema zai murmure kafin wasan, bayan da bai buga fafatawar da suka yi da Malaga ba ranar Asabar.

Mai tsaron bayan Madrid Marcelo ba zai buga karawar ba, sakamakon dakatar da shi da aka yi, Fabio Coentrao ne zai maye gurbinsa.

A karawar farko da suka yi a Atletico Madrid ta shi wasa aka yi babu ci.