Zan ci gaba da horar da Munich — Guardiola

Pep Guardiola
Image caption Munich za ta karbi bakuncin FC Porto ranar Talata a gasar cin kofin zakarun Turai

Pep Guardiola ya ce zai ci gaba da horar da Bayern Munich wasan kwallon kafa, duk da rade-radin da ake yi zai bar kulob din.

A karshen kakar wasan badi ne kwantiragin Guardiola da Munich zai kare, wanda ake hasashen zai koma gasar Premier kuma a Manchester City.

Guardiola ya lashe kofin Bundesliga da kofin kalubale a shekarar farko da ya horar da 'yan wasan Munich, kuma a bana ma yana fatan yin hakan.

Munich ce ke kan gaba a gasar Bundesliga a bana da maki 73 kuma za ta buga wasan daf da karshe a kofin kalubale da Borussia Dortmund mako mai zuwa.

Ranar Talata ne kuma za ta buga wasa na biyu da FC Porto a gasar cin kofin zakarun Turai, a wasan farko da suka buga a Portugal 3-2 aka doke Munich.